OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ƴan Bindiga Sun Sace Mutum Bakwai Ƴan Uwan Juna A Katsina

Ƴan Bindiga Sun Sace Mutum Bakwai Ƴan Uwan Juna A Katsina

The gumen went from house to house waking their victims before leading them to the bushes

A daren jiya Talata, wayewar Laraba ne wasu yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka sace mutane bakwai ‘yan gida daya a garin kabomo dake karamar hukumar bakori a jihar Katsina.

Wasu daga ‘yan uwan wadanda iftila’in ya rutsa da su sun bayyana cewa yan bindigar sun shigo suna harbe harbe kafin su tafi da mutanen.

Yan bindigar sun shiga garin ne a jiya da misalin karfe daya na dare inda sukayi sukayi harbe harbe a sama.

Bayan sun tabbatar da gama tsorata mutane da harbe-harben ne suka fara shiga gidaje, inda suka dauki mutane bakwai yan uwan juna.

Cikin wadanda suka sace har da mata uku masu ɗauke da juna biyu, lamarin da ya kara firgita alumar yankin.

Hajiya Amina kabir wacce abin ya faru akusa da gidanta ta shaidawa Premier Radio yadda suka tsinci kan su cikin firgici a daren.

Kawo yanzu dai babu labarin ko sun nemi kudin fan sa, sai dai ana kyautata zaton zasu tuntubi yan uwan wadanda aka sace din.

Wasu daga cikin jahohin arewa sun dade suna fuskantar barazanar yan bindiga tare da masu garkuwa da mutane ciki kuwa har da jihar katsina wacce ke daya daga wadanda suka fi illatuwa da hare haren.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci