OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane Hudu Da Ƙona Gidaje A Ƙauyukan Benue

Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane Hudu Da Ƙona Gidaje A Ƙauyuk

Rahotanni sun ce an kashe mutane hudu a wasu hare-hare da wasu da ake zargin makiyaya ne suka kai kan wasu ƙauyuka biyu a karamar hukumar Guma ta jihar Benue. 

A rahoton da jaridar Punch ta ruwaito tace makiyayan da ake zargi sun kona gidaje da dama a yankin.

Idan za'a tunawa makon jiya ne aka kashe mutane tara a wasu hare-hare a karamar hukumar Guma da wasu da ake zargin makiyaya ne.

A hare-haren na baya bayan nan da suka auku a ranar Juma’a da sanyin safiyar Asabar, mazauna yankin sun cewa, wadanda ake zargin makiyaya ne sun mamaye al’ummomi da dama tare da kashe mutane hudu.

An bayar da rahoton cewa an kashe mutane uku a unguwar Yogbo ranar Juma’a sannan kuma an kashe wani a unguwar Ukohol da sanyin safiyar Asabar.

Wani dan yankin da ya nemi a sakaya sunansa saboda fargabar harin, ya ce, “An kashe mata biyu a bayan makarantar firamare ta Yogbo da wata guda kuma a jiya Jumma’a. 

A jiya Asabar maharan sun kashe mutum daya a Ukohol, Sun kuma kona gidaje da dama a kauyuka da dama da aka kai hari a yankin.

Yayin da aka ruwaito cewa mazauna al’ummomin da abin ya shafa sun gudu saboda fargabar sake kai hari.

Da yake tabbatar da hare-haren, Shugaban karamar hukumar Mike Ubah, ya ce an kashe mutane hudu a hare-haren.

Shugaban ya bayyana haka ne a wani kauye a ranar Asabar, “An kashe mutane hudu, Uku daga cikinsu a Yogbo yayin da aka kashe daya a Ukohor a cikin lokaci guda."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci