OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ambaliyar ruwa: Mutane 37 sun mutu, 171,000 sun rasa matsugunan su a Adamawa

Ambaliyar ruwa: Mutane 37 sun mutu, 171,000 sun rasa matsugu

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Adamawa (ADSEMA) ta tabbatar da mutuwar mutane 37 sakamakon ambaliyar ruwa a jihar.

Hukumar ta kuma tabbatar da cewa mutane 171,000 ne ambaliyar ta raba da matsugunan su.

A cewar sakataren zartaswar hukumar, Dr Muhammad Sulaiman, mutane 58 ne suka jikkata yayin da hekta 89,000 na gonaki suka nutse a cikin ruwa.

Sulaiman ya bayyana cewa ya shafi dukiyoyin gwamnati da na masu zaman kansu wadanda suka hada da makarantu, asibitoci, kasuwanni, gidaje da wuraren ibada, wanda hakan ya shafi harkokin tattalin arziki da zamantakewa.

Ya koka da cewa ambaliyar ta wuce yadda hukumomin Najeriya suka yi hasashe wanda ya tsaya ne kawai ga jama'ar da ke gabar kogin Benue a jihar.

Ya ce hukumar ta raba kayan agaji ga daukacin sansanonin guda 10 da aka kafa domin ‘yan gudun hijira bisa umarnin gwamnan jihar, Ahmadu Umaru Fintiri.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci