OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Fintiri ya kaddamar da hanya mai tsawon kilomita 2.5 a Girei

Fintiri ya kaddamar da hanya mai tsawon kilomita 2.5 a Girei

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya kaddamar da titin Njobbore mai tsawon kilomita 2.5 na Vunoklang a karamar hukumar Girei na jihar.

Gwamnan ya ce aikin da aka fara watanni takwas da suka gabata, wata hanya ce ta kare zaizayar kasa sakamakon ambaliyar ruwa da mazauna yankin suka fuskanta a baya.

Fintiri ya kuma yi godiya ga jama’a bisa addu’o’i da goyon bayan da suke ba gwamnatin sa.

Ya kuma kara jaddada kudurin sa na kyautata rayuwa ga jama'a.

Yayin kaddamar da hanyar a yau, Fintiri ya samu rakiyar mataimakin sa, Crowther Seth da wasu manyan jami'an gwamnati.

A nasa jawabin, kwamishinan ayyuka da makamashi na jihar, Adamu Atiku ya yaba wa gwamnan bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen bunkasa ababen more rayuwa a jihar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci