OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Zamu kama dakatar da iyaye daga shiga cibiyoyin gudanar da jarabawa- JAMB

Zamu kama dakatar da iyaye daga shiga cibiyoyin gudanar da j

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta bayar da umarni ga duk masu cibiyar jarabawar ta kwamfuta (CBT) da su tsare duk iyayen da aka samu a harabar wuraren aikinsu a lokacin da ake rubuta jarabawar UTME ta 2024.

 

Magatakardar JAMB, Farfesa Isaq Oloyede ne ya bayar da umarnin a wani taron tattaunawa da masu gudanar da cibiyar jarabawar CBT. 

 

A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar ta JAMB, Dakta Fabian Benjamin ya fitar, yace matakin na da nufin hana iyaye tsoma baki ko kawo cikas a wajen gudanar da jarrabawar. 

 

Hakazalika, duk dalibin da iyayensu suka karya wannan ka'ida suka kutsa kai cikin dakin jarabawar za a dakatar da shi daga rubuta jarabawar.

 

Sanarwar ta kara da cewa an gano cewa shishigin da iyaye sukeyi yayin gudanar da jarabawar yana tallafawa tabarbarewar jarrabawar.

 

 “Wannan matakin ya zama dole domin bincike ya tabbatar da akasarin lokuta iyayen dake zuwa dakin jarabawar sukan kawo cikas wajen yanda ake gudanar da ita. Wasu bata-garin kuma suna badda kama a matsayin iyaye domin su kutsa kai cikin cibiyoyi su lallata alamura” in ji sanarwar.

 

 Sanarwar ta kuma jaddada bukatar daukar tsauraran matakai don dakile wadannan laifuffuka, jami'an tsaro za su hada kai da masu CBT don tabbatar da gudanar da ayyukansu cikin sauki.

 

Bugu da kari, sanarwar ta jaddada cewa dole ne dalibi ya cika shekaru 17 kafin su zauna jarrabawar saboda haka babu bukatar iyayensu su rakosu cibiyar rubuta jarabawar.

 

 An shirya gudanar da jarrabawar a cibiyoyin CBT 700 a duk fadin kasar, tare da tanade-tanade don magance duk wata matsala ta fasaha da ka iya tasowa. 

 

Idan har aka samu tarzoma, za a dage zaman jarabawar zuwa wata ranar a nan gaba yayin da za'a dakatar da dukkan dalibin da ya kawo cikas ko iyayensu suka kawo cikas daga rubuta jarabawar.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci