OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

‘Yan sandan sun kama wasu ‘yan fashi da makami 19 a Katsina

‘Yan sandan sun kama wasu ‘yan fashi da makami 19 a Kats

The Police said the arrest was possible through credible Intel

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wasu mutane 19 da ake zargin ‘yan fashi da makami ne a jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Idris Dauda-Dabban ne ya bayyana hakan a wata zantawa da manema labarai a yau (Laraba) a Katsina.

Dauda-Dabban ya ce rundunar ta samu nasarar kwato motoci 13 da wadanda ake zargin suka sace.

A cewar sa: “Za a iya tunawa, a kwanakin baya, mazauna yankin cikin garin Katsina, sun gamu da aika-aikan gungun da ta kware wajen fasa gidaje, fashi da makami da satar motoci.

“Rundunar ba ta huta ba, amma ta kaddamar da farautar ’yan fashin da ikon Allah kuma ta yi nasarar murkushe ‘yan kungiyar da ke addabar jihar.

“An kama mutane 19 da ake zargin ‘yan kungiyar ne, ciki har da shugaban su, sannan an samu wasu motoci 13 da ake zargin na sata ne daga hannun su.

“A ranar 31 ga watan Yuli, ‘yan kungiyar sun kai farmaki gidan wani Nura Lawal na Modoji Quarters, GRA, Katsina, da bindiga da sauran makamai,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ta ruwaito.

Dauda-Dabban ya kara da cewa, wadanda ake zargin sun yi wa Lawal din fashin mota kirar Toyota Corolla L.E 2010, kudi N340,000 da kuma kayan sa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci