OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Yan Sandan Legas Sun Kama Sojan Da Ya Sokawa Dan achaba Wuka

Yan Sandan Legas Sun Kama Sojan Da Ya Sokawa Dan achaba Wuka

Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta kama wani Kofur din Soji na bataliya ta 159 a Yobe bisa zarginsa da soka wa wani Dan achaba wuka a ciki.

 Kakakin rundunar ‘yan sandan SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kama sojan a ranar Litinin.

 Hundeyin ya bayyana cewa an tsare sojan ne a ranar Asabar da misalin karfe 3 na safe a unguwar Ikorodu da ke Legas. 

A cewar sa, a ranar Asabar sun samu bayani daga wani mai gadin wani gurin sayar da giya da misalin karfe 2 na dare cewa sojan da aka sakaye sunan sa ya caka wa wani dan achaba mai suna Saheed Isa wuka.

 A cewar Hundeyin, lamarin ya faru ne bayan sojan da marigayin suka samu sabani kan wani batu da ba a tantance ba Inda a garin fadan marigayin ya samu munanan raunuka.

 “Jami’an ‘yan sanda na sashin sun ziyarci wurin da lamarin ya faru, inda aka garzaya da shi zuwa asibiti domin kula da lafiyarsa, a halin yanzu an kwantar da shi kuma yana karbar magani.” inji shi.

 An kama wanda ake zargin da wukar da ya aikata laifin da ita kuwa a halin yanzu ana cigaba da gudanar sa bincike.

 A hannu guda kuma, rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta bayyana shirin gurfanar da mutane sama da 1,019 a gaban kotu bisa laifuka da dama. 

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai a Legas ranar Lahadi. 

A cewar Hundeyin, an kama wadanda ake zargin ne a ranar 8 ga watan Afrilu da karfe 1:15 na rana da kuma Afrilu 14th da misalin karfe 12:50 a yayin sumamen da aka kai guraren da ake aikata fasadi a fadin jihar.

 Za a gurfanar da su a gaban kuliya, bisa laifukan da suka hada da mallakar makamai da alburusai, fashi da makami, kai wa fararen hula hari, da kuma mallakar haramtattun kwayoyi da dai sauransu.

 Kakakin ya ce jami’an Yan sanda za su ci gaba da kai samame a sassa daban-daban na jihar, inda ya yi gargadin cewa masu ra’ayin aikata laifuka su guji zuwa Legas ko kuma suyi kaura idan har suna jihar. 

Ya kuma yabawa jama’a bisa ga bayanan da suka bai wa ‘yan sanda kan ayyukan wadanda aka kama, inda ya yi kira da su cigaba da tallafa musu da irin wadannan bayanan sirrin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci