OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

‘Yan Majalisa Sun Tsige Kakakin Majalisar Jihar Filato

‘Yan Majalisa Sun Tsige Kakakin Majalisar Jihar Filato

‘Yan majalisar dokokin jihar Filato guda takwas sun tsige shugaban majalisar dokokin jihar, Nuhu Abok.

Da sanyin safiyar Alhamis ne ‘yan majalisar wakilai daga jam’iyyar APC mai mulki suka tsige shi cikin zauren majalisar cikin tsauraran matakan tsaro.

Majalisar ta kuma nada mamba mai wakiltar mazabar Pengana, Yakubu Sanda a matsayin sabon shugaban majalisar.

Sai dai kuma an hana ’yan jam’iyyar adawa ta PDP shiga harabar majalisar.

Haka kuma an dauki matakin rufe harabar majalisar da kuma hanyoyin da ke kusa da ita.

An dauki matakin ne don hana tashin hankali.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci