OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gobara Ta Ƙona Ginin Majalisar Dokokin Jihar Kogi

Gobara Ta Ƙona Ginin Majalisar Dokokin Jihar Kogi

Kogi State House of Assembly

Wata gobara da ta tashi da sanyin safiya ta ƙone harabar majalisar dokokin jihar Kogi dake unguwar Crusher a Lokoja.

Gobarar ta ratsa rufin dakin mahalisar, inda ta yi ɓarna mai tarin yawa.

Kakakin majalisar, Mathew Kolawole, da mai baiwa jihar shawara kan harkokin tsaro, Kwamanda Jerry Omodara, na daga cikin waɗanda suka fara zuwa harabar majalisar.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, babu wani bayani dangane da dalilin gobarar.

Shugaban Majalisar ya ce yana zargin zagon ƙasa ne amma ya gaza gane inda matsalar ta fito.

Da aka tambaye shi ko gobarar nada alaƙa da abin da ya faru tsakanin Majalisar da kungiyar Dangote, sai ya ce hakan ya rage ga jami’an tsaro su tantance.

"Ya kamata mu bar jami'an tsaro su yi aikin su kuma su ba mu rahoto." in ji kakakin.

Sai dai wata majiya ta ce ya yi zargin fashewar wani abu ne amma ba zai iya cewa wane ne ke da alhakin hakan ba, cewar Jaridar Punch.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci