OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yajin Aiki: ASUU Ta Daukaka Kara A Shari'arta Da Gwamnatin Tarayya

Yajin Aiki: ASUU Ta Daukaka Kara A Shari'arta Da Gwamnatin T

ASUU Strike

Kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ta garzaya kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja, inda ta bukaci ta yi watsi da hukuncin da kotun masana’antu ta kasa, (NIC)ta yanke na janye yajin aikin da ta shafe watanni bakwai tana yi.

Kungiyar, a cikin daukaka kara 14 da ta shigar ta hannun tawagar lauyoyin ta karkashin jagorancin wani dan rajin kare hakkin bil’adama, Femi Falana, SAN, ta kuma bukaci a dakatar da aiwatar da hukuncin.

Idan za'a iya tunawa, a hukuncin da kotun masana'antu ta yanke a ranar Larabar da ta gabata ta bakin mai shari’a Polycarp Hamman, ta umurci malaman jami’o’in da ke yajin aikin da su koma bakin aiki, har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan karar da gwamnatin tarayya ta shigar ta hannun lauyanta, James Igwe.

Justine Hamman yayin zartar da hukuncin ya ce wannan hukunci zai amfani duka bangarorin biyu don amfanin kasa da kuma saboda masu karatun digiri a kasar da ke gida tun ranar 14 ga Fabrairu.

Ya ce yajin aikin na da illa ga daliban jami’o’in gwamnati wadanda ba za su iya zuwa manyan makarantu masu zaman kansu ba.

Abin jira a gani shine, yanayin hukunci da kotun daukaka kara zata zartar game da karar da aka shigar gabanta.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci