OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yajin Aiki: Gbajabiamila Ya Nemi Ganawa Da ASUU

Yajin Aiki: Gbajabiamila  Ya Nemi Ganawa Da ASUU

Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya rubuta wasika zuwa ga kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) inda ya bukaci ganawa da kungiyar a ranar Talata, 20 ga watan Satumba.

Wasikar na dauke da sa hannun magatakardar majalisar wakilai Yahaya Danzarta, kuma an aiketa ga shugaban kungiyar ASUU.

Wasikar mai ɗauke da kwanan  watan Satumba 15, 2022, na cewa: “Hon. Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila  yana gayyatar ku zuwa taron masu ruwa da tsaki don neman mafita mai dorewa kan yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta fara tun a watan Fabrairun 2022.

Gbajabiamila a cikin wasikar ya bayyana damuwarsa kan yadda tattaunawar gwamnatin tarayya da kungiyar  ta kasa cimma ruwa.

 Majalisar wakilai ta damu matuka game da sabon yajin aikin da ake ganin ya bijirewa duk wani yunkuri da aka yi na neman mafita ko cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayya da malaman jami’o’in da ke yajin aikin.

Majalisar ta damu matuka da mummunan sakamakon yajin aikin ga ingancin ilimin matasan mu da aka ajiye a gida tsawon watanni shida da suka gabata duk da tsoma bakin majalisar da wasu ‘yan Najeriya da dama domin ganin an warware lamarin.

Dangane da abubuwan da suka gabata, majalisar ta sake neman wata dama ta sake haduwa da masu ruwa da tsaki da shugabannin kungiyar ASUU don neman sulhu cikin lumana ba tare da la’akari da cewa lamarin ya riga ya shiga kotun masana’antu ba.”

 An kuma bukaci ASUU a cikin wasikar da su gabatar da rubutaccen ra’ayinsu game da lamarin ga majalisar kafin ranar taron.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci