OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yajin Aiki : Majalissar wakilai zata gana da kungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya ASUU

Yajin Aiki : Majalissar wakilai zata gana da kungiyar malama

Majalisar wakilai za ta gana da kungiyar malaman jami’o’i,  da sauran masu ruwa da tsaki domin nemo mafita ga yajin aikin da kungiyar ta shafe watanni tana yi.

Sanarwar na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren majalisar wakilai Yahaya Danzaria ya fitar ranar Litinin a Abuja. Ya ce taron zai gudana ne a ranar Talata a zauren majalisar wakilai ta kasa.

Ya bayyana cewa taron da zai gudana tsakanin kungiyar ta ASUU da sauran masu ruwa da tsaki za ayi shine domin nemo mafita mai dorewa kan yajin aikin da ASUU ta shiga tun watannin baya.

A cewarsa, majalisar ta damu matuka da yajin aikin da malaman suka sake tsindima wanda hakan ya sake lalata duk wani yunkuri da aka yi na ganin an magance matsalar.

Ya kara da cewa majalisar ta damu da cewar an kasa cimma matsaya tsakanin gwamnatin tarayya da malaman jami’o'i da ke yajin aikin.

Ya ce majalisar ta damu matuka game da abinda yajin aikin zai haifar ga matasa.

Ya ce an ajiye dalibai a gida tsawon watanni shida duk da shige da ficen da masu ruwa da tsaki sukayi don ganin an shawo kan matsalar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci