OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yajin aiki: Majalisar Wakilai za ta gabatar da sabuwar yarjejeniyar da aka kulla da ASUU ga shugaba Buhari

Yajin aiki: Majalisar Wakilai za ta gabatar da sabuwar yarje

'Yan majalisar wakilai za su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari domin gabatar da sabuwar yarjejeniyar da suka kulla da kungiyar malaman jami'o'i (ASUU).

Shugaban majalisar, Femi Gbajabiamila ne ya sanar da hakan a ranar Talata, bayan wata ganawa data gudana tsakanin ‘yan majalisar da kungiyar ASUU da kuma wakilan gwamnatin tarayya.

Taron wanda ya sami halartar shugabannin kungiyar ASUU karkashin jagorancin shugabanta, Emmanuel Osodeke, da kuma wakilin gwamnatin tarayya karamin ministan ilimi Goodluck Opiah, da ‘yan majalisar dokoki.

Mista Gbajabiamila, bayan ganawar sirri da aka yi a harabar majalisar dokokin, ya ce tawagar malaman sun gabatar da batutuwa bakwai, kuma an cimma matsaya.

Ko da dai bai bayyana cikakken bayanin yarjejeniyar ba, kakakin majalisar, ya bayyana cewa ‘yan majalisar za su gabatar da yarjejeniyar ga shugaba Buhari yayin da kungiyar ta ASUU itama za ta sanarwa sauran mambobinsu matsayar da aka kulla.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci