OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yajin Aiki: Kotu Ta Bukaci Gwamnati Da ASUU Su Warware Takaddamar Su A Wajen Kotu

Yajin Aiki: Kotu Ta Bukaci Gwamnati Da ASUU Su Warware Takad

ASUU

A jiya ne babbar kotun daukaka kara ta Abuja ta bukaci gwamnatin tarayya da mambobin kungiyar malaman jami’o’i ASUU da ke yajin aiki da su warware takaddamar da ke tsakaninsu a wajen kotu.

 Hakan yasa kwamitin alkalai ukun da suke sauraron karar suka dage sauraron karar da kungiyar ASUU ta shigar gabanta na tsawon sa’o’i 24.

 Kotun ta yanke shawarar ne don ba wa bangarorin da ke rikici da juna damar sake tunani da nufin warware dukkan matsalolin da ke damun su cikin ruwan sanyi.

 Mai shari’a Georgewill Biobele Abraham ya bukaci lauyan gwamnatin tarayya, James Igwe, SAN, da lauyan ASUU, Femi Falana, SAN, da su karfafawa wadanda suke wakilta gwiwar su rungumi kishin kasa wajen samar da masalahar da zai ci da kasar gaba.

 A nasa bangaren, Falana, SAN, ya ce kungiyar ASUU a kodayaushe kofarsu a bude take domin tattaunawa, inda ya ce tun da farko ya fara yunkurin daukar matakin sulhu.

Falana ya kuma jaddada cewa matukar ana son a samu sulhu to sai bangarorin biyu sun shirya haduwa a tsakiya wajen cimma bukatun su. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci