OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Wasu da ake zargin makiyaya ne sun kutsa kauyen Benue, sun kashe mutum 5

Wasu da ake zargin makiyaya ne sun kutsa kauyen Benue, sun k

Bayan wani hari da wasu da ake zargin makiyaya ne suka kai a kauyen Yelwata da ke karamar hukumar Guma a jihar Benue, an kashe mutane biyar.

An kai harin ne da tsakar ranar Laraba.

Wani mazaunin kauyen mai suna Orduen ya bayyana wa jaridar Punch cewa maharan sun kutsa kauyen ne da misalin karfe 1:00 da rana a yau (Laraba) yayin da suka harbe mutane a gonakin su.

A cewar sa: “Makiyaya ne da suka afka wa kauyen mu a Yelwata da misalin karfe 1 na rana a yau.

“Sun far wa mutane da dama da ke aiki a gonar su da bindiga da adduna.

“Yayin da suka gama barnan sai suka gudu zuwa cikin daji, wasu daga cikin wadanda suka jikkata sun shiga cikin jama’a domin su sanar da mu.

“A lokacin da matasa suka je neman mutanen mu da suka je gona, mun gano gawarwakin mutane biyar da suka ji raunuka, kuma an kai su asibiti domin yi musu magani."

Rundunar ‘yan sandan jihar Benue ta bakin kakakin ta, SP Catherine Anene ita ma ta tabbatar da faruwar lamarin.

Anene ta ce tuni aka tura jami’an rundunar ‘yan sandan zuwa yankin.

A cewar ta: “An tabbatar da harin da aka kai a kauyen Yelwata.

“Jami’an ‘yan sandan da aka tura yankin na ci gaba da gudanar da aiki. 

"Za a bayyana cikakkun bayanai da zarar an kammala aikin."

Mai bada shawara kan harkokin tsaro a yankin, Waku Christopher, wanda ya yi magana a madadin shugaban karamar hukumar, Mike Uba ya ce an kashe mutane biyar yayin da hudu suka jikkata.

A cewar sa: “Gaskiya ne, makiyaya da manoman ne, an kai wa manoma biyar hari a gonakin su aka kashe su, mutane uku ko hudu kuma sun samu rauni."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci