OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ƙungiyar Yarbawa ta Arewa Ta Yiwa Tinubu Alƙawarin Ƙuri’u Miliyan 20

Ƙungiyar Yarbawa ta Arewa Ta Yiwa Tinubu Alƙawarin Ƙuri�

APC Presidential Candidate, Bola Ahmed Tinubu

Dai dai lokacin da zaɓen 2023 ke ƙara ƙaratowa, ƙungiyar Yarbawa ta Arewa Agenda ga Tinubu ( NOYAT), ta tabbatarwa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu kuri’u miliyan 20.

Ƙungiyar ta kuma yi masa alƙawarin ba da goyon baya ba tare da ɓata lokaci ba don tabbatar da shi a matsayin shugaban ƙasa.

Ƙungiyar ta ce suna da hanyoyin sadarwa a faɗin jihohin Arewa 19 da suka haɗa da Babban Birnin Tarayya, kuma tuni aka samar da wani tsari na wayar da kan ƴan ƙasa a kan hakan.

Da yake jawabi yayin taron zaman lafiya da addu’o’i na musamman da aka shirya wa Bola Tinubu, ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna a APC, Sanata Uba Sani da kodinetan kungiyar na kasa, Hon.  AbdulRasheed Adekeye ya bayyana irin goyon bayan da ƙungiyar ke baiwa Tinubu da Shettima.

A cewar kodinetan na ƙasa, matsayin NOYAT na goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya ta’allaka ne da ƙa’idoji da aƙida ba bisa ƙabilanci ba.

“Mun kafa tantin mu tare da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu bisa gaskiya da adalci kamar yadda Gwamnonin APC na Arewa suka rigaya suka nuna shi.”

“Mun yi imani da iyawar Tinubu da Shettima, kuma hakan ya faru ne saboda abubuwan da suka yi a jihohin Legas da Borno a matsayin gwamnoni.

"Ba mu taɓa yin shakku kan iyawar Tinubu da Shettima na jagorantar ƙasar nan ba, zuwa wani matsayi da zai biya buƙatun ƴan Najeriya," in ji Adekeyele, cewar Jaridar Vanguard.

Don haka ya yi ƙira ga ƴan Nijeriya da su goyi bayan burin shugaban kasa na Tinubu, ya ƙara da cewa ƴan Nijeriya kada su bari ƴan siyasa masu son kai su yi amfani da su, wadanda ba su da wata manufa ta alheri ga ƙasar nan.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci