OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Sojojin Najeriya Sun Musanta Wata Alaƙa Da Makiyaya, Ƴan Fashi

Sojojin Najeriya Sun Musanta Wata Alaƙa Da Makiyaya, Ƴan F

Army Sets Up New Base As COAS Fetes Troops To Sallah Luncheon

Rundunar sojin Najeriya ta musanta ikirarin cewa jami’anta na hada kai da makiyaya da ‘yan fashi da makami domin addabar yankin Gabashin kasar da kuma jihar Benuwe.

Rundunar ta bayyana irin wadannan ikirari a matsayin shirme da cin mutunci, da nufin bata sunan rundunar.

A wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar ranar Asabar ya ce wadannan labarai na ƙungiyoyi baza suyi kashe wa rundunar gwiwa ba.

Sanarwan ta ce, "Rundunar sojojin Najeriya tasa mu wani labari na batanci, zage-zage da kuma batanci daga wata ƙungiya mai suna International Society for Civil Liberty and Rule of Law, suna zargin sojojin Najeriya, na aiki da makiyaya/'yan fashi domin addabar yankin Gabashin kasar nan da jihar Benue.

“Hakan na jawo ɓata suna na rundunar, yayin da ake haɓaka ƴan sa-kai, ƙungiyoyin da ba su da doka da doka, cewar Jaridar Punch.

“Abin takaici ne ga wadannan ‘yan ta’adda, kokarin da sojojin Najeriya ke yi na nuna kishin kasa da rashin gajiyawa wajen kare martabar yankin da Nijeriya abu ne da kowa ke gani da karfin gwiwa kuma ya samu yabo daga kasashen duniya.

Ya kara da cewa rundunar ta gudanar da atisaye ba wai a jihohin Kudu maso Gabas kadai ba, har ma a duk jihohin tarayyar kasar nan, wanda hakan ya rage yawan aikata laifuka.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci