OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Shugaban Yan Bindiga Ya Yi Barazanar Ramako Bayan Kashe Mutanen Sa A Benue

Shugaban Yan Bindiga Ya Yi Barazanar Ramako Bayan Kashe Muta

Bayan wani samame da dakarun sojin Najeriya suka kai, an samu nasarar kashe ‘yan bindiga hudu a karamar hukumar Katsina-Ala ta jihar Benue.

An kawar da ‘yan bindigar ne a wani artabu da dakarun Operation Whirl Stroke (OPWS) na sojojin Najeriya a ranar Talata.

Shugaban ‘yan bindigar da ke addabar kauyukan, Terna Gide ya yi barazanar kai harin ramuwar gayya a kauyukan karamar hukumar.

Shugaban karamar hukumar Kastina-Ala, Alfred Atera ya tabbatar da wannan barazanar yana mai cewa Gide ya aika barazanar ga kauyukan.

A yayin da yake zantawa da Jaridar Daily Trust, Atera ya bayyana cewa, “An kawar da hudu daga cikin ‘yan bindigar, an lalata musu sansanin su tare da kayan tsafi, Terna Gide yana barazanar daukar fansa.

“Tun safiyar yau (Laraba), ya kira yana barazanar cewa zai yi fiye da abin da aka lalata a sansaninsa.

"Ya kira lambar wayar daya daga cikin masu gadin sa kai don ba da barazanar."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci