OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Adamawa Ta Bada Bayani Bayan Rikicin Kabilanci

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Adamawa Ta Bada Bayani Bayan Ri

Nigerian Police

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta ce sakamakon rikicin da ya barke tsakanin al’ummomin Lunguda da Waja na karamar hukumar Lafiya-Lamurde, an samu zaman lafiya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Sulaiman Nguroje ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na NAN a Yola.

Nguroje wanda ya yi magana a ranar Litinin ya ce lamarin ya faru ne da safiyar Litinin.

Ya kara da cewa rundunar ta yi gaggawar yunkurawa bisa rahotannin rikicin tare da tura mutanenta yankin domin dawo da zaman lafiya.

Nguroje ya ce, “Kwamishanan ‘yan sanda, Sikiru Akande, ya aika da tawagar ‘yan sandan mobile da ke yaki da kisan-kiyashi zuwa yankin, kuma kamar yadda a halin yanzu an samu daidaito."

Ya kuma bayyana cewa ba a gama tattara adadin wadanda suka mutu ba saboda ana ci gaba da bincike.

Yayin da yake tabbatar da cewa rundunar ta yi kokari wajen tabbatar da tsaron lafiyar mutane, ya bukaci matafiya da su cigaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Kabilun sun dade suna takun saka tsakanin su kan filayen noma.

Idan dai za a iya tunawa, AllNews ta ruwaito gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya ziyarci karamar hukumar Balanga da ke kan iyaka da jihar Adamawa, inda ya yi kira da a kwantar da hankula tsakanin al’ummar Lunguda da Waja.

Ya nuna rashin jin dadinsa kan sabon rikicin da ya barke tsakanin al’umomin.

Ya kara da cewa gwamnatin sa za ta bi diddigin wadanda suka aikata ta’asar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci