OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Mutane Miliyan 2 Sun Rasa Matsugunan su Sanadiyar Ambaliyar Ruwa a Delta, Bayelsa Da Rivers

Mutane Miliyan 2 Sun Rasa Matsugunan su Sanadiyar Ambaliyar

Gwamnatin tarayya a jiya ta bayyana cewa kawo yanzu ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 603 tare da raba mutane 1,302,589 da muhallan su tare da lalata sama da kadada 108,393 na gonaki a fadin kasar nan.

 

 Hakazalika, gwamnatin ta bayyana cewa, iftila'in ya raunata mutane 2,407, ya kuma lalata wani bangaren gidaje 121,318, ya kuma ruguza gidaje 82,053 baki daya, sannan ya lalata kadada 108,392 na gonaki, sannan ya shafe kadada 332,327 na gonaki baki daya a fadin kasar nan.

 

 Da take bayyana wadannan alkaluman yayin wata ganawa da manema labarai a Abuja, ministar harkokin jin kai, kula da bala’o’i da ci gaban jama’a, Hajiya Sadiya Umar-Farouq, ta yi hasashen cewar akwai yiwuwar karuwar barnar ruwan nan gaba a jihohin Anambra, Cross Rivers, Ribas, Delta da Bayelsa.

Ta kuma bukaci gwamnatocin jihohin su yi kokarin kwashe mazauna yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa zuwa wasu guraren domin gujewa asarar rayuka da dukiyar al'umma.

 

 Da yake tsokaci game da mummunar illar ambaliyar ruwa a jiharsa, gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri a jiya ya bukaci gwamnatin tarayya da ta ayyana dokar tabaci ta kasa kan iftila'in.

 

 Gwamna Diri, wanda ya yi wannan roko a wani taron gaggawa na majalisar tsaro da aka yi a Yenagoa, ya ce maudu’in taron shi ne tattaunawa da shugabannin hukumomin tsaro daban-daban domin tantance halin da ake ciki a dunkule da kuma lalubo hanyoyin da za a dakile illar ambaliyar ruwan.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci