OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Mutane Bakwai Sun Mutu A Rikicin Kamfanin Ɗangote Da Gwamnati 

Mutane Bakwai Sun Mutu A Rikicin Kamfanin Ɗangote Da Gwamna

Aliko Dangote

Aƙalla ma’aikata bakwai ne suka mutu a kamfanin siminti na Dangote sakamakon rikici akan filin kamfanin.

Rikicin ya faru ne a ranar Laraba da ta gabata a harabar kamfanin dake Obajana a jihar Kogi.

Rahotanni sun bayyana cewa an harbe wasu  har lahira a yayin wata arangama tsakanin jami’an tsaron jihar da ma’aikatan kamfanin.

Hakan ya faru ne a lokacin da aka a mamaye harabar kamfanin bisa umarnin gwamnatin jihar.

A cewar sanarwar da Babban Manajan Sadarwa na Kamfanin na Kamfanin Dangote, Sunday Esan ya fitar, ƙungiyar ta ƴan banga ta samu jagorancin Darakta-Janar na Filaye na Jiha, Kwamishinan Ma’adanai na Kasa, da kuma Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamna kan Harkokin Tsaro, Jerry Omodara. 

Da take mayar da martani, gwamnatin jihar ta ce majalisar dokokin jihar Kogi ta bayar da umarnin rufe kamfanin bayan binciken da ta gudanar kan aikin masana'antar siminti da ake zargin an gano cewa babu wani sahihin takardu na sayan filin kamfanin.

Majalisar dokokin jihar ta yi zargin cewa Dangote, bisa gayyatar da majalisar ta yi masa, ya bukaci ƙarin lokaci amma bai bayyana a zauren majalisar ba domin ya nuna wata hujjar saɓanin hakan.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Kingsley Fanwo, ya ce bisa ga tsarin mulkin majalisar dokokin jihar Kogi, da kuma karar da al’ummar jihar Kogi suka shigar, an gudanar da bincike kan kamfanin na Obajana. 

“An gano cewa babu wani sahihin takarda ta sayen filin da aka yi, saboda Dangote bai nuna shaidar abin da aka biya ba a matsayin shaidar sayan.

“Yan majalisar sun gayyaci shugaban kamfanin Aliko Dangote a gaban majalisar domin yin bayani amma ya kasa bayyana a gaban majalisar jihar inda yayi ta ba da uzuri.

"Saboda haka, majalisar ta ba da umarnin rufe kamfanin har zuwa lokacin da suka gabatar da shi tare da ingantacciyar shaida ta sayen filin."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci