OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yobe: Kifewar Kwale-kwale Yayi Sanadin Mutuwar Mutum Biyu Da Bacewar Wasu Da Dama

Yobe: Kifewar Kwale-kwale Yayi Sanadin Mutuwar Mutum Biyu Da

Boat Mishap

Biyo bayan hatsarin kwale-kwale da ya afku a karamar hukumar Tarmuwa da ke jihar Yobe, an bayyana cewa nutum biyu sun mutu yayin da wasu da dama suka bace.

Kakakin gwamnan jihar , Mamman Mohammed ne ya bayyana hakan.

Mohammed ya bayyana cewa hatsarin ya afku ne a sanadiyyar ambaliyar ruwa inda wasu kwale-kwale guda biyu dauke da fasinjoji a hanyar su ta zuwa kasuwar Babangida a ranar Asabar da yamma Suka kife.

Ya kuma bayyana cewa kifewar kwale-kwalen ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu.

Ya kuma kara da cewa, gwamna Mai Mala Buni ya nuna alhininsa kan lamarin.

Premium Times ta ruwaito cewa an yi nasarar tsinto gawarwakin mutum biyu, yayin da har yanzu ba a san adadin fasinjojin da hatsarin ya rutsa da su ba.

Mohammed ya kara da cewa, tun daga lokacin ne gwamnan ya bayar da umarnin cewa hukumomin da abin ya shafa su yi azamar gudanar da bincike mai zurfi don gano sauran wadanda abin ya shafa.

Ya kuma shawarci matafiya a kan hanya musamman matafiya kan ruwa da su yi hattara.

Ya ba da umurni cewa duk waɗanda suke zaune akan hanyoyin ruwa su ƙaura su bar wurin don gudun faruwar irin wannan lamari.

A cewar sanarwar, gwamna Buni ya ce: “Ruwan sama mai karfi da ambaliya suna tahowa ne daga nesa ba tare da an san da zuwan su ba; ya kamata a ko da yaushe mu kasance cikin shiri tare da kauce wa hanyoyin ruwa masu hatsari."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci