OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Majalisar Dokoki ta Sake Mika Kudirin Dokar Zabe, Tana Jiran Amincewar Buhari

Majalisar Dokoki ta Sake Mika Kudirin Dokar Zabe, Tana Jiran

Majalisar dokokin Najeriya ta mika wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kudirin dokar zabe da aka sake gyara domin amincewar sa.

 

Magatakardar Majalisar, Olatunde Amos Ojo ne ya mika takardun kudirin dokar da aka sake gyara a ranar Litinin.

 

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin majalisar dattawa, Sanata Babajide Omoworare ne ya bayyana hakan.

 

Omoworare ya ce hakan ya yi daidai da tanadin kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

 

A cewar sa, ana samun hakan a cikin “Sashe na 58 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) da kuma Cap. A2 LFN 2004.”

 

Shugaban a ranar 19 ga watan Nuwamba na 2021 ya ki sanya hannu a kan kudirin da aka mika masa.

 

Da yake bayyana ci gaban, Omoworare ya bayyana cewa, "Bayan haka majalisar dokokin kasar ta sake yin aiki akan Kudirin zaben, sannan kuma majalisar dattawa da ta wakilai sun amince da haka a ranar 25 ga watan Janairun 2022."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci