Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar NNPP, yayi kira ga gwamnati kan gyaran hanyoyin sufuri da suke kaiwa gabar ruwan teku dake Apapa, Jihar Legas.
Kwankwaso, yayi kiran ne a yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar karkashin jagorancin, Prime Maritime Project.
Dan takarar ya bayyana cewa karsar nan na da bukatar yin shirye-shirye na bunkasa fannonin samar da kudaden shiga musamman, fannin sufurin jiragen ruwa.
A cewar sa: "Na saurari bayanan ku, kuma na fahimci kalubale dake tattare da bangaren sufurin jiragen ruwa a Najeriya.
"Babban misali shine hanyar da ta dangana da gabar ruwa ta Apapa, wanda a wata ziyara dana sami zarafin kawo jihar Legas na gani cinkushe da motocin diban kaya a daidai gadar Ijora dake hanyar.
"A matsayi na wanda ya rike mukamin matekamakin shuagaban majalisar wakilai ta kasa, gwamnan jiha, da kuma na tsohon minista a Najeriya ina da zummar kawo sauyi a fannin abinda ya shafi tsaro, cin hanci da rashawa, da hukumomin tsaro daban-daban dake kasar nan," kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.
Shima a jawabin sa, wanda ya jagoranci taron, Kunle Folarin, ya bukaci dan takarar da ya cika alkawurran da yayi ta hanyar kawo gagarumin sauyi a fannin sufurin jiragen ruwa da kasuwanci, wanda aka mai da saniyar ware a ayyuka da gwamnatin Najeriya ke yi.
0 Tsokaci