OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Ku Guji Siyasar Cikin Gida, Cewar Shugaban NYSC Ga 'Yan Bautan Kasa

Ku Guji Siyasar Cikin Gida, Cewar Shugaban NYSC Ga 'Yan Baut

Darakta-Janar na masu yi wa kasa hidima (NYSC), Brig. Janar Shaibu Ibrahim ya gargadi ‘yan bautan kasa da su daina shiga harkokin siyasar garin da aka tura su.

Ibrahim ya yi wannan gargadin ne a sansanin Nnamdi Azikwe dake jihar Anambra yayin bikin rufe kwas na 2021 Batch C stream 1.

Ko’odinetan jihar Anambra, Misis Yetunde Baderinwa wadda ta yi magana a madadin shugaban hukumar ta ce yayin da suke mu'amala da al’umma, “Siyasa wuri ne ba na zuwa ba”.

Ya bayyana cewa, "Bisa ga manufar shirin, ana sa ran ku shiga cikin al'ummomin da kuke karbar bakuncin , tare da godiya da mutunta al'adunsu. Duk da haka, dole ne in jaddada cewa tsunduma cikin siyasar yankinsu ba wurin shiga ba ne a gare ku.'

Shugaban hukumar ya kuma yabawa 'yan bautan kasan bisa shiga cikin shirin koyon sana’o’i da hukumar NYSC ta shirya.

Ana gudanar da horon ne a sansanonin dake fadin kasar nan karkashin shirin NYSC Skill Acquisition and Entrepreneurial Development (SAED).

Ya kuma shawarce su da su yi amfani da damar da suke da su wajen kara samun ilimin sana'o'in hannun. 

Ya kuma kara da cewa hukumar ta NYSC na hada kai da sauran cibiyoyin kudi domin samar da rance ga ‘yan bautan kasan.

Ya kuma gargade su da su guji abin da ka iya cutar da su saboda matsalolin tsaro da ake fama da su.

Yayin da yake ba su tabbacin kariyar gwamnati, ya gargade su da su daina tafiye-tafiyen dare.

Ya ce shirin yana hada gwiwa da jami’an tsaro a jihar domin tabbatar da tsaron su.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci