OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kotu Ta Tabbatar Da Umahi a Matsayin Ɗan Takarar Sanatan Ebonyi Ta Kudu

Kotu Ta Tabbatar Da Umahi a Matsayin Ɗan Takarar Sanatan Eb

Wata kotun ɗaukaka ƙara dake zamanta a Abuja ta tabbatar da gwamnan Ebonyi, David Umahi a matsayin sahihin zabaɓɓen ɗan takarar jam’iyyar APC.

Gwamna yana wa'adin sa ne na ƙarshe kafun ya nemi takarar sanata na Ebonyi ta kudu a zaɓe mai zuwa.

Ann Agom-Eze ya kalubalanci fitowar Umahi a matsayin ɗan takarar kujerar Sanata na jam’iyyar APC.

Yayin da kotun ta amince da Umahi a matsayin sahihin ɗan takaran na jam'iya mai mulki ta APC.

Ann ya maka Umahi ne a kotu bisa zargin cewa zaɓen na cike da kura kurai kuma ba'a bisa ƙa'ida ba.

A wani labarin kuma, mun kawo muku rahoton cewa a ranar Laraba kotu ta tabbatar da Bashir Machina a matsayin sahihin ɗan takaran sanata a yankin Yobe ta arewa.

Machina wanda ya shigar da ƙarar ya samu nasara ne akan abokin hamayyan sa wato shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan.

Daga bisani kuwa, bayan hukuncin kotun, Ahmad Lawan yace bazai ɗaukaka ƙara ba kuma ya amince da hukuncin kotun.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci