OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnatin Tarayya Ta Sako Wasu da Ake Zargin Yan Kungiyar IPoB Ne

Gwamnatin Tarayya Ta Sako Wasu da Ake Zargin Yan Kungiyar IP

An sako wasu mutane uku da ake zargin 'yan haramtacciyar  kungiyar awaren IPoB, bayan sun shafe shekaru biyu da rabi a Barikin sojan  Ohafia, a jihar Abia.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International a Najeriya ce ta bayyana hakan a ranar Alhamis.

Kungiyar kare hakkin da ta yi imani da ‘yanci, adalci da daidaito, ta kuma yi kira ga hukumomin Najeriya da su bayar da bayanai game da matsayin sauran wadanda aka tilastawa bacewar su.

Sanarwar ta ce: “Amnesty International na farin ciki da sakin Sunday Nwafor, mai shekaru 59, Uzonwanne Ejiofor mai shekaru 48, da Wilfred Dike, mai shekaru 36, wadanda jami’an sojojin Najeriya suka kama a ranar 27 ga Fabrairu, 2020 a jihar Abia.

Sakin nasu ya biyo bayan kamfen na Amnesty International da kiraye- kirayen neman 'yancinsu.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta bukaci mahukuntan Najeriya da su bayar da bayanai game da halin da sauran wadanda aka kama aka tsare suke ciki ba tare da boye-boye ba.

Kungiyar ta kuma bukaci a baiwa iyalansu da lauyoyinsu damar ganinsu, ko gurfanar da su a kotu, ko kuma a sake su daga tsarin da aka yi musu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci