OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yan Awaren IPOB Sun Musanta Sanya Dokar Zama a gida A Ranar Talata

Yan Awaren IPOB Sun Musanta Sanya Dokar Zama a gida A Ranar

Kungiyar Yan Awaren IPOB sun ce ba za a yi zaman gida a ranar Talata 4 ga watan Oktoba ba, saboda shugabanta Nnamdi Kanu ba zai gurfana a gaban kotu a ranar ba.


Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun IPoB, Comrade Emma Powerful, ya fitar Inda ya bayyana cewar raderadin  za'a cigaba da sauraron karar Nnamdi Kanu a birnin tarayya a ranar hudu ga watan oktoba ba gaskiya bane.

Yace saboda haka yan kabilar igbo ba sai sun zauna a gida ba a wannan rana kamar yanda suka saba a duk sanda Nnamdi Kanu zai bayyana a gaban kotu.


Sanarwar ta IPOB ta kara da cewa, “A ranar 4 ga Oktoba, 2022, rana ce da IPOB za ta shigar da kara domin  kalubalantar  karya dokar da gwamnatin Najeriya ta yi wajen sace shugabanmu Nnamdi Kanu daga kasar Kenya zuwa Najeriya ba bisa ka'ida ba"

 

 "Dole ne gwamnatin Najeriya ta bayar da shaida ga duniya kan yadda da kuma dalilin da ya sa suka yi kwato shugabanmu Mazi Nnamdi Kanu zuwa Najeriya, a babbar kotun Umuahia dake jihar Anambra " A cewar sanarwar.

 

 Sanarwar ta kuma Kara da cewar jagorancin IPOB zai hukunta dukkan wanda yake yada jita-jita game da dokar zaman gidan.

 

IPOB ta bukaci duk wani dan kasar Biafra na gida da na kasashen waje ya yi watsi da irin wadannan jita-jita.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci