OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Shugaba Buhari Ya Yi Umarnin Gurfanar Da Wadnda Suka Kashe Sojoji Gaban Kotu

Shugaba Buhari Ya Yi Umarnin Gurfanar Da Wadnda Suka Kashe S

Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari bayyana kaduwa bisa samun labarin harbe wani jami'in soja da wata abokiyar zamansa sannan aka fille musu kai a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

 

Shugaba Buhari, wanda ya yi Allah wadai da wannan mummunan al’amari, kuma kuma umarci hukumomi da su gaggauta gurfanar da wadanda suka aikata laifin gaban kotu.

 

Mahukuntan kasar nan na zargin kungiyar ‘yan aware ta Biafra, wato IPOB da kashe ma’auratan a lokacin da suke tafiya daurin aurensu a karshen makon jiya.

 

Kungiyar dai ta musanta hannu a kisan.

 

'Yan bindiga a kudu maso gabashin kasar nan na ci gaba da zafafa kai hare hare kan jami’an tsaro a kokarin sun a bijirewa gwamnati.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci