OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnatin Tarayya Ta Daga Darajar Ma'aikatan Hukumar NSCDC, TA Kashe Gobara Da Wasun Su.

Gwamnatin Tarayya Ta Daga Darajar Ma'aikatan Hukumar NSCDC,

Nigeria Security and Civil Defense Corps (NSCDC)

Gwamnatin tarayya ta kasa, ta daga darajar ma'aikatan hukumar farin kaya ta, Civil Defense, hukumar shige da fice ta Customs da hukumomin; gidajen gyaran hali, da ta kashe gobara a fadin kasar nan.

Mai magana da yawun hukumar dake kula da ayyukan gamayyar hukumomin ta kasa, ACP Paul Abraham ya cewa, hakan ya bayyana ne a wata sanarwar cikin gida wacce tafito daga hannun kwanturola-janar na gamayyar hukumomin ta kasa, Injiniya Jaji Abdulganiyu a yau.

Abraham ya kara da cewa, sanarwar ta bayyana daga darajar ma'aikata 363, da kuma ma'aikata 2,019 da aka daga likafar su zuwa matakin sufritanda na hukumar kare gobara a mataki na daya da kuma matakin sufritanda.

A yayin taya ma'aikatan murnar samun sabbin matsayi a hukumomin, shugaban gamayyar hukumomin na Customs, Civil Defense, Fire Service, Correctional da Immigration, Jaji Abdulganiyu ya yabawa ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola da ma'aikatan kan kwazo da suka nuna wajen yin ayyukan su a fadin Najeriya. 

 

DT

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci