OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnatin Legas Tace Ambaliyar Ruwa Na Yiwa Jihar Barazana

Gwamnatin Legas Tace Ambaliyar Ruwa Na Yiwa Jihar Barazana

Gwamnatin jihar Legas a jiya ta sanar da mazauna jihar musamman mazauna gabar kogin Ogun da su tashi.

 Gwamnatin jihar ta kuma umurci dukkan wadanda suke da gidaje ko suke tsaka da yin gini da su tabbatar sun bi matakai da tsare-tsare da gwamnati ta gindaya na samar da gine-gine a fadin jihar.

 A bangaren kogin Ogun, kwamishinan muhalli da albarkatun ruwa, Tunji Bello, wanda ya bayar da sanarwar jan kunnen, ya jaddada bukatar mazauna yankin su yi taka tsantsan.

Bello ya ce lamarin na iya kara tabarbarewa sakamakon sako ruwa daga madatsar ruwa ta Oyan da shugabannin hukumar raya kogin Ogun-Oshun suka yi wanda ya kara yawan ruwa a tafkin.

 Ya lissafo yankunan da suke hasashen ambaliyar ruwa zata iya shafa: Ketu, Alapere, Agric, Owode Onirin, Ajegunle, Alagbole, Kara, Isheri Olowora, Araromi Otun Orisha al’ummar, Agiliti, Maidan, Mile 12, Odo Ogun, Owode Elede, Agboyi 1, Agboyi. II, Agboyi III.

 Ya ce: “Gwamnatin jihar kuma tana aiki tare da hadin gwiwar hukumar raya kogin Ogun Oshun don tabbatar da cewa fitar da ruwa daga madatsar ruwa bata kawo barazana ba ga mazauna yankin.”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci