OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Gwamnatin Jihar Borno Ta Samar Da Kekune 6, 000 Domin Karfafawa Yara Zuwa Makaranta Akan Lokaci

Gwamnatin Jihar Borno Ta Samar Da Kekune 6, 000 Domin Karfaf

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum| Hoto Daga: Guardian

 

Gwamnatin Jihar Borno ta bayar da kekuna dubu shida ga wasu daga cikin daliban makarantun jeka-ka-dawo dake kauyuka domin karfafa musu gwiwar zuwa makaranta a akan lokaci.

 

Kwamishinan Ilimi a jihar, Abba Wakilbe ne ya sanar da hakan a ranar Laraba yayin taron bude makarantar fasaha ta sakandare a Wuyo dake karamar hukumar Bayo a jihar. Wakilbe ya ce makarantar sakandiren fasaha ta Wuyon ta samu kekune 300 domin a rabawa daliban da zasu zo makarantar daga  makwabtan kauyuka. Ya kara da cewa gwamnati ta kuma samar da littafan karatu 231,000 a fadin jihar.

 

Kwamishinan ya cigaba da cewa, a cikin shekaru biyu da Babagana Zulum ya zamo gwamna a jihar, an samar da manyan makarantu guda 21, wanda hudu daga cikin su, na koyon fasaha ne.

 

Da yake nasa jawabin, Gwamna Zulum ya bayar da umarnin samar da kayayyakin koyo a dakunan koyon gwaje-gwaje na makarantun fasahar domin su zamo daidai da zamani. Haka kuma gwamnan ya bayar da umarnin daukar kwararrun malamai domin cigaban koyo da koyarwa.

 

Da yake jawabin maraba, shugaban karamar hukumar Bayo, Mohammad Biryel, ya yabawa gwamnati bisa kawo makarantar karamar hukumar sa. Biryel y ace hakan zai taimaka wajen magance rashin ilimi a yankin, kuma zai taimakawa wajen bawa matasa ilimin dogaro da kai.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci