OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Gwamnati Ta Bada Hutun Kwanaki 2 Don Bikin Sallah Da Ranar Ma'aikata

Gwamnati Ta Bada Hutun Kwanaki 2 Don Bikin Sallah Da Ranar M

Minister of Interior, Ogbeni Rauf Aregbesola| Photo Source: The Guardian

Gwamnatin tarayya ta bayar da hutun kwanaki biyu domin bikin ranar ma’aikata na shekarar 2022 da kuma bikin karamar sallah a fadin kasar nan.

Kwanaki biyun da aka bayar sun hada da Litinin 2 ga watan Mayu da kuma Talata 3 ga watan Mayu na 2022. 

An bayyana hakan ne a wata sanarwa da babban sakatare a ma’aikatar harkokin cikin gida, Dr Shuaib Belgore ya fitar.

Sanarwar wadda ta fito a daren Alhamis ta bayyana cewa ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya.

Da yake yaba wa ma'aikata a duk fadin kasar, Aregbesola ya ce ma'aikatan "Su ne babban alhakin daukakar kasar." 

Ya kuma taya daukacin al’ummar musulmi murnar ganin karshen watan Ramadan mai alfarma.

Ya bukaci musulmi da su yi koyi da kyawawan halaye na Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wa Sallam).

Ya ci gaba da cewa, “Kada ayi watsi da Kamun kai da sadaukarwa da ke tattare a lokacin azumi, a kiyaye da inganta shi, domin zama nagartaccen mutum kuma mai ibada na gaskiya."

Ministan ya kuma tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa nan ba da jimawa ba kalubalen tsaro zai zama tarihi, inda ya kara da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dukufa wajen kawo karshen matsalolin tsaro.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci