OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

BUK Ta Yi Rashin Farfesa Olofin

BUK Ta Yi Rashin Farfesa Olofin

Emeritus Professor, Emmanuel Ajayi Olofin|

Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) ta yi rashin wani farfesa mai suna Emmanuel Ajayi Olofin mai shekaru 80 a duniya.

Olofin, dan asalin Ijero na jihar Ekiti ya rasu ranar Talata.

Ya kasance malami a Sashen Geography na BUK kafin rasuwarsa.

Marigayin tsohon dalibi ne a jami’ar Ibadan inda ya sami digiri na farko a fannin geography. 

Ya yi digirinsa na biyu (Msc) a jami’ar Malaya ta kasar Malaysia kafin ya yi balaguron neman digiri na uku a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Wasu daga cikin makarantun da ya karantar sun hada da Jami’ar Najeriya, Nsukka, Jami’ar Obafemi Awolowo, Ife, Jami’ar Malaya da Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Ya kuma ci lambar yabo ta Commonwealth Scholarship Malaysian tsakanin 1970-1972 da USAID Grant for Interfaith Dialogue a 1991.

Ya kuma kasance memba na International Geographical Union da Malayan Geological Society daga 1970 zuwa 1972.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci