OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Borno: Zulum Ya Nada Sabon Akanta Janar

Borno: Zulum Ya Nada Sabon Akanta Janar

Borno state governor, Babagana Umara Zulum| Photo Source: PremiumTimes

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya nada Baba Bura Usman a matsayin sabon Akanta Janar na jihar.

Kakakin gwamnan, Malam Isa Gusau ne ya bayyana hakan a daren Laraba a cikin wata sanarwa.

A cewar sanarwar, Usman ya kasance Daraktan ajiya a ma’aikatar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta jihar Borno, tun a shekarar 2020 kafin sabon nadin.

Gusau ya kara da cewa sabon Akanta Janar din yana da gogewar sama da shekaru 20 akan harkokin kudi da sarrafa su.

Usman ya karbi mulki daga hannun Mai Adamu Ya’u wanda ya yi ritaya kwanan nan.

A cewar sanarwar: “Akantan Janar din ya kasance tun a shekarar 1990, ya yi aiki a matsayin Mataimakin Akanta a wani kamfani mai zaman kansa, Premier Property Dev Co. Ltd, kafin ya koma ma’aikatan gwamnatin jihar Borno a matsayin babban Akanta da aka tura zuwa majalisar fasaha da al’adu ta jihar Borno a Maiduguri, a shekarar 1998."

Usman kuma mamba ne na kungiyar Akantoci ta kasa (ANAN).

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci