OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Borno: Kungiyar Matuka Keke Napep Ta Karbi Bakoncin Kwamishinan Sufuri

Borno: Kungiyar Matuka Keke Napep Ta Karbi Bakoncin Kwamishi

Borno State Commissioner for Transportation, Dr Abubakar Tijjani

Kungiyar matuka Keke Napep a jihar Borno, ta karbi bakuncin kwamishinan sufuri na jihar, Dr Abubakar Tijjani a unguwar Gwange dake Maiduguri.

Kwamishinan wanda kungiyar ta gayyace shi domin taronta na shekara ya bayyana irin tallafin da Gwamna Babagana Umara Zulum ya baiwa matukan.

Da yake jawabi ga kungiyar, kwamishinan ya ce Zulum ya zuba Naira biliyan 1.5 ga matuka Keke Napep da nufin samar da ayyukan yi a jihar.

Ya kuma yi kira gare su da su goyi bayan ci gaban gwamnatin Zulum a matsayin wani mataki na mayar da martani ga kokarin gwamnan.

Tijjani ya kuma yi kira ga matukan da su kasance masu bin doka da oda yayin da suke gudanar da harkokin su na kasuwanci tare da tallafa wa hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Borno (BOTMA) wajen gudanar da ayyukan su.

Ya kuma yi kira gare su da su baiwa hukumar hadin kai kan lamarin sa fitillar cikin Keke Napep din, inda ya ce duk wanda aka samu ba tare da fitulun ciki ba, za a hukunta shi.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa gwamna Zulum ya yi alkawarin bayar da tallafin naira miliyan dari da za a raba wa mutane dubu hudu na masu tuka Keke Napep.

Matukan da suka yaba wa gwamna Zulum ta hannun shugaban gamayyar kungiyoyin matuka Keke Napep na jihar, Hon Maikano Mohammed Bundur sun bayyana cewa Zulum ya tallafa musu da Keke Napep 500 da mota kirar Corolla LE 100 a kan wani tallafi na aro.

Daga karshe ya yaba wa gwamnan bisa tallafawa mambobin kungiyar 1000 da naira miliyan hamsin.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa kungiyar matuka Keke Napep za ta ci gaba da mara wa APC baya a zaben 2023 mai zuwa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci