OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Babu Abinda Yakai Kiwon Lafiya Tsada a Najeriya – Osinbajo

Babu Abinda Yakai Kiwon Lafiya Tsada a Najeriya – Osinbajo

Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya ce kudaden da ake kashewa a fannin kiwon lafiya a Najeriya yayi yawa duk da dimbin kasafin kudi a fannin.

Mista Osinbajo ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a cikin jawabinsa na musamman a taron kaddamar da manufofin ci gaba mai dorewa SDG-3 da SDG-4.

Mista Osinbajo ya ce dole ne Najeriya ta ɗinke barakar da ke tsakanin kasafin kiwon lafiya da kuma kudaden da ake kashewa a fadin kasar.

Mataimakin shugaban kasar ya ce rahotannin sun kawo karshen wani dogon aiki da aka fara tun a watan Disambar 2018 a taron karawa juna sani na yankin Afirka kan tsarin SDG a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Mista Osinbajo ya ce da amincewa da ajandar da kuma tsarin SDGs, Najeriya ta tsara wa kanta hangen nesa na kawo karshen talauci da kuma bayar da gudunmowa wajen kare duniya nan da shekarar 2030.

“Samar da ci gaba mai ɗorewa, manufa ce da ta yi daidai da muradin gwamnatinmu na fitar da mutane miliyan 100 daga kangin talauci cikin shekaru 10.

“Saboda haka ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa wasu tsare-tsare don tallafa wa ci gaban nasarar da aka samu na SDGs.

“Ofishin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan SDGs, ya ci gaba da ba da jagoranci na fasaha wajen aiwatar da SDGs.

Ya kara da cewa rahoton ya bayyana bukatar magance gibin tsari da kalubalen da ake fuskanta a fannin kiwon lafiya da ilimi, cewar Jaridar Daily Nigerian.

“Binciken da ke ƙunshe a cikin waɗannan dabarun kimantawa ya ƙarfafa shaidar inganta kiwon lafiya da sakamakon ilimi a Najeriya.

"Kuma nuna yadda duk masu ruwa da tsaki, gwamnatoci, abokan ci gaba da kungiyoyin farar hula za su iya magance gibin tsarin da kalubale."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci