OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

ASUU Ta Yi Watsi Da Umarnin Mahukuntan Jami'ar Nassarawa Na Komawa Bakin Aiki

ASUU Ta Yi Watsi Da Umarnin Mahukuntan Jami'ar Nassarawa Na

Ƙungiyar malaman jami’o’i reshen jami'ar Jihar Nasarawa da ke Keffi, ta sha alwashin ci gaba da yajin aikin kungiyar na kasa.

Hakan na zuwa ne bayan mahukuntan makarantar sun bayar da umarnin a  koma makaranta, cewar Jaridar Punch.

Da yake yiwa manema labarai jawabi a ranar Juma’a a Keffi, shugaban ASUU reshen jami'ar, Dakta Samuel Alu, ya bayyana umarnin hukumar gudanarwar a matsayin wani shiririta da kuma cin amana.

Ya sha alwashin cewa ba za a tilasta wa malaman jami’ar komawa bakin aiki ba, ba ba tare da son ransu ba.

"Ƙungiyar ta saba da barazana, cin zarafi da farfagandar da wasu ɓangarori ke yi game da gwagwarmayar.

“Don kaucewa shakku, ASUU daya ce, Don haka, ba za a iya ganin ASUU a NSUK tana gudanar da ayyukan ta daban da sauran rassan ASUU ba.

"Tana aiki ne cikin cikakken bin umarnin sakatariyar kasa," in ji shi.

Alu ya nuna rashin jin daɗinsa da yadda mahukuntan jami’ar suka bayar da wannan umarni da sanin cewa ASUU ta daukaka kara kan hukuncin da kotun masana’antu ta ƙasa ta yanke.

“Bisa la’akari da abubuwan da aka ambata, tilasta wa malaman jami’o’in komawa aji ya zama haramun da rashin mutunta doka da za a iya fassara ta a matsayin wulakanci ga kotu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci