OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

ASUU: Gwamnatin Najeriya ta umurci shugabannin jami’o’i da su bude makarantu

ASUU: Gwamnatin Najeriya ta umurci shugabannin jami’o’i

Gwamnatin tarayya ta umarci shugabannin jami’o’i da su bude makarantu domin baiwa dalibai damar komawa bakin karatun su.

Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda da ta fito a yau litinin a garin Abuja mai dauke da sa hannun daraktan kudi da asusun kula da jami’o’in kasar NUC, Sam Onazi, a madadin babban sakataren hukumar Farfesa Abubakar Rasheed.

Takardan dai an aikata ne ga dukkan shugabannin jami'o'i, mataimakansu tare da shugabannin majalissar gudanarwar na jami’o’in gwamnatin tarayya, in da aka umurce su da su bude makarantu.

“Ku Tabbatar kun de makarantu an fara laccoci; a cigaba da ayyuka kamar yadda aka saba a dukkanin jami'o'i", cewar takardar.

In ba a manta ba kungiyar ASUU ta shiga yajin aikin ne tun ranar 14 ga watan Fabrairu domin matsawa don a inganta jami’o’in da kuma kudaden kula, da batun albashin malaman jami’o’i da dai sauransu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci