OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ana Sa Ran Atiku Zai Karbi Tsohon Gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau Zuwa PDP

Ana Sa Ran Atiku Zai Karbi Tsohon Gwamnan Kano, Ibrahim Shek

Rahotanni daga Kano sun bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, na shirin karbar Ibrahim Shekarau a jam'iyyar NNPP zuwa jam'iyyar sa.

Bayanai na nuni da cewa ana sa ran tsohon mataimakin shugaban kasar zai dawo daga Landan inda  zai isa jihar Kano dan karbar  Shekarau a hukumance, inji rahoton The Cable.

An bayyana cewa ganawar Atiku da tsohon dan gwamnan jihar kanon zai kasance ne a ranar Lahadi 28 ga watan Agusta.

Wata majiya ta ce za'a yi  taron ne domin ganin Shekarau ya shiga cikin tawagar yakin neman zaben Atiku da kuma jagorantar yunkurin samun gagarumin goyon baya daga yankin arewa maso yamma kafin 2023.

"An dai amince da yarjejeniya tsakanin Shekarau da Atiku inda zai ziyarce shi a gidansa na Kano ranar Lahadi don neman goyon bayansa a kan takararsa ta shugaban kasa".

"Malam a matsayinsa na tsohon dan takarar shugaban kasa kuma babban jigo ne a siyasar Kano, don haka ne dan takararmu ya yanke shawarar sauka kano domin neman goyon bayansa," in ji majiyar.

Kawo yanzu dai babu wani jigo daga ɓangaren PDP ko NNPP da ya tabbatar da haka, amma a makon da ya gabata, an jiyo Shekarau na cewa jagoran jam'iyyar NNPP kuma ɗan takarar shugaban kasar jam'iyyar a zaɓen baɗi, Rabi'u Musa Kwankwaso ya yaudare shi tare da ƙin cika masa alkawuran da ya ɗaukar masa yayin komawar sa jam'iyyar daga APC.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci