OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Zaben 2023: Bidiyon Tinubu yana motsa jiki ya bayyana don karyata rade-radin rashin lafiyar sa

Zaben 2023: Bidiyon Tinubu yana motsa jiki ya bayyana don ka

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya fitar da wani faifan bidiyo na yadda yake gudanar da atisayen motsa jiki.

Ya fitar da faifan bidiyon ne domin ya karyata jita-jitar da ake yadawa kan rashin lafiyar sa.

Mista Tinubu, wanda ya shafe kusan mako guda a kasar waje, ya fitar da bidiyon ta shafin sa na Twitter tare da rubuta taken "Ina cikin koshin lafiya".

“Da yawa sun ce na mutu; wasu kuma su na cewa na janye daga yakin neman zaben shugaban kasa.

"Toh..ba haka bane lafia ta kalau “Wannan ita ce gaskiyar magana: Ina da ƙarfi, ina cikin koshin lafiya kuma a shirye nake in yiwa 'yan Najeriya hidima daga zarar na karbi mulki.

#BAT23 .

Mista Tinubu ya bar Najeriya zuwa kasar Birtaniya ne a ranar 24 ga watan Satumba, wanda hakan ya kara rura wutar hasashe kan dalilan tafiyar ba zato ba tsammani.

Tawagar yakin neman zabensa ta ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ya tafi zuwa kasar Burtaniya ne domin samun hutu kafin a fara yakin neman zaben.

An kuma ce ya yi tafiyar ne domin ganawa da wasu kungiyoyi da ba a bayyana sunayensu ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci