OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yaro Mai Watanni Bakwai Na Cikin Mutane Biyar Da Suka Rasu Sakamakon Kifewar Kwale-Kwale A Jigawa

Yaro Mai Watanni Bakwai Na Cikin Mutane Biyar Da Suka Rasu S

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da rasuwar wani jariri mai watanni bakwai, da wasu  mata hudu bayan kifewar kwale-kwalen su a hanyar su ta dawowa gida.


Kakakin rundunar, DSP Lawan Shiisu ya tabbatarwa wakiliyar mu haka yau Laraba cewa, lamarin ya faru ne a yammacin Talata.


DSP Shiisu yace masunta sun samu nasarar tsamo gawarwakin mata biyu da jaririn, inda daga bisani aka samo sauran gawarwakin mutum biyun.


Jami’in ya bayyana sunayen wadanda suka rasu da Oneyaniwura Kasagama mai shekaru 50, da Lafiya Bulama mai shekaru 40, Badejaka Kasagama, mai shekaru 40.

Sauran sun hada da Gimto Kasagama, mai shekaru 40 and jariri Mai Madu Bulama mai watanni bakwai.


Karo na uku ke nan ana samun rasuwar mutane sakamakon kifewa ko nutsewar kwale-kwale a Jigawa, inda mamakon ruwan da ake fama da shi ke ta’azzara lamarin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci