OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

‘Yan Najeriya Zasu Tsunduma Cikin Talauci Muddin Aka Cire Tallafin Man Fetur, Cewar Abdulsalami

‘Yan Najeriya Zasu Tsunduma Cikin Talauci Muddin Aka Cire

Janar Abdulsalami Abubakar| Hoto Daga: Guardian

A ranar Alhamis din da ta gabata ne tsohon shugaban kasan Najeriya, Abdulsalami Abubakar ya nuna damuwar sa kan cire tallafin man fetur.

Tsohon shugaban kasan yace duba da yadda kasar ke fama da matsaloli daban-daban, cire tallafin zai kara dagula lissafi.

Gwamnatin tarayya ta ce tana shirin dakatar da biyan tallafin man fetur nan da watan Yuni amma wasu masu ruwa da tsaki da suka hada da kungiyar kwadago ta Najeriya sun yi watsi da matakin.

Abdulsalami yace sama da mutane miliyan tamanin ne ke fama da talauci a halin yanzu.

Ya kuma bayyana hakan a matsayin abin da ke ruruta matsalar tsaro.

A cewar sa, “A zahiri, yanzu Najeriya na fuskantar matsalar karancin abinci da ke tattare da annobar COVID-19 a duniya da kuma ‘yan bindiga a jihohi da dama a Arewacin Najeriya."

Ya kara da cewa, "kamar yadda gwamnati ta tsara, za ta jefa miliyoyin mutane cikin talauci."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci