OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Kudin Tallafin Man Fetur: NNPC Na Bukatar Naira Tiriliyan 3 a 2022

Kudin Tallafin Man Fetur: NNPC Na Bukatar Naira Tiriliyan 3

Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta biya naira tiriliyan 3 a matsayin tallafin man fetur na 2022.

A halin yanzu naira biliyan 445 ne ke Iya samuwa daga watan Janairu zuwa Yuni kamar yadda kasafin kudin 2022 ya bayyana.

Hakan yazo ne cikin bayanin Ministar kudi da tsare-tsare, Zainab Ahmed, yayin zantawa da manema labarai a Abuja.

Bayanin nata yazo ne jim kadan da aka gudanar da taron majalisar zartarwa ta tarayya na mako-mako a fadar shugaban kasa, Muhammadu Buhari a ranar Laraba.

Zaku tuna cewa a ranar Litinin din da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin ta na cire tallafin man fetur din. 

Ministar ta bayyana cewa kimanin Naira Tiriliyan 3 ne ake bukata don cigaba da bada tallafin man fetur din.

A cewar ta, "Mun kuma gabatar wa majalisar zartarwan a yau bukatar neman karin kudade don ba mu damar biyan karin tallafin man fetur a cikin kasafin kudin 2022."

“Za ku tuna cewa a cikin kasafin kudin 2022 kamar yadda aka tsara, mun samar da Naira biliyan 443 domin bayar da tallafi daga watan Janairu zuwa Yuni.

“Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ya gabatar wa ma’aikatar kudin bukatar Naira Tiriliyan 3 a matsayin tallafin mai na shekarar 2022. Abin da hakan ke nufi shi ne, sai mun kara samar da Naira Tiriliyan 2.557 domin samun damar biyan tallafin da ake bukata, wanda ya kai kusan Naira biliyan 270 a kowace wata.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci