OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnati Na Kashe Biliyan 18.39 A Tallafin Man Fetur Kullum- Ministar Kuɗi

Ministar kudi da tsare-tsare, Zainab Shamsuna Ahmad tace ma'aikatar ta na biyan kamfanonin saida man fetur masu zaman kansu naira triliyan 6.219 na kuɗin tallafin man fetur tsakanin shekarar 2013 zuwa 2021.

Ta bayyana hakan ne yayin taron kwamitin binciken tallafin man fetur da majalisar wakilai ta kafa wadda Ibrahim Aliyu ke jagoranta.

Ministar kuɗin ta bayyana cewar gwamnatin tarayya a kullum tana kashe akalla biliyan 18.397 a tallafin man fetur ɗin.

Ta bayyanawa kwamitin binciken cewar gwamnatin bazata iya ci gaba da ɗaukar nauyin tallafin man fetur din ba, saboda haka bayar da shawarar gudanar da taron masu ruwa da tsaki domin a samar da mafita.

Taron zai hada da Shugaban Majalissar dattijai, jam'iyun siyasar kasar nan da sauran waɗanda abun ya shafa domin yanke hukunci akan cigaba ko barin tsarin tallafin man fetur din baki daya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci