OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Muna Kashe Fiyeda Biliyan 18 Akan Tallafin Mai A Kullum – Minista

Muna Kashe Fiyeda Biliyan 18 Akan Tallafin Mai A Kullum –

Minstar kudi a Najeriya, Hajiya Zainab Ahmed ta bayyana cewa gwamnati na kashe naira 283 akan kowace lita ko kuma naira biliyan  18.397 a kowace rana a matsayin tallafi.

Bayanin na zuwa ne bayan Kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai da ya binciki tsarin bayar da tallafin man fetur daga shekarar 2013 zuwa 2022, a ranar Alhamis.

Komitin ya tuhumi ministar akan kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa, a kan biyan tallafin da ake yi wa Premium Motor Spirit (na man fetur) da Gwamnatin Tarayya ke biya.

 A yayin da take bayani, ministar ta ce, “A shekarar 2023, hasashen da aka yi shi ne cewa matsakaitawar babbar motar da za ta fita a rana za ta kai Naira miliyan 64.96 a kowace rana;  wato kusan miliyan 65 a kowace rana, ana amfani da matsakaicin farashi a kasuwar akan kudi naira 448.20 sannan kuma farashin famfo mai N165 akan kowace lita. 

"Wannan yana ba mu matsakaiciyar murmurewa, wato bambanci tsakanin N165 da naira 448 na naira 283.2

 “Saboda haka, kawai a ninka adadin lita a kowace rana, farashin canjin Naira na kasuwa zuwa dala, sannan, tazarar da ke tsakanin farashin famfo da farashin kasuwar, adadin tallafin da ake bayarwa a kowace rana ya kai naira biliyan 18.397.
 
 “Don haka, idan za ku yi duba a shekara, daga Janairu zuwa Disamba, zai zama naira tiriiliyan 6.715.  

"Idan kuma na tsawon rabin shekara ne zai zama kashi 50 cikin 100 na wannan tiriliyan 3.375. 

"Na ce a baya a shawarwarin da muka aika wa majalisa domin tantancewa kan MTEF rabin shekara ne, zai kai tiriiliyan 3.357.”

Ministan ta ci gaba da cewa, “raran mai shi ne banbancin farashin famfo wanda a yanzu an kayyade shi akan Naira 165 (kowace lita) da kuma farashin saukan da muke yi a kan Naira 448 a kowace lita a shekarar 2023. Ko a yanzu kudin ya kusa haka.  .

 “Don haka, tallafin PMS da muke dauke da shi yau a kasar nan ya kai kusan Naira 283 kan kowace lita;  abin da muke dauke da shi kenan.  Don haka, shi ne bambancin farashin famfo da farashin sauka da man fetur a kasar nan.”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci