OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

'Yan Najeriya Miliyan 25 Ne Ke Fama Da Yunwa A Najeriya—Masani

'Yan Najeriya Miliyan 25 Ne Ke Fama Da Yunwa A Najeriya—Ma

Manoma

Shugaban wata kungiyar masana, da masu bincike kan abinci a kasar nan, Farfesa Kola Matthew Anigo, ya ce akwai ’yan Nijeriya kimanin milyan 25 da yanzu haka ke fama da yunwa.

Ya bayyana haka a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, lokacin da yake jawabin bude taron kungiyar karo na 52 a Lahadin nan.

Masanin ya ce kasar nan ce ta daya a Afrika, kuma ta biyu a duniya wajen yawan masu fama da rashin wadataccen abinci, kuma ya danganta haka ga ayyukan ‘yan bindiga da sauran kungiyoyin ‘’yan ta’adda a kasar.

Da yake tofa albarkacin bakin sa kan batun, wani mai bincike kan al’amuran tsaro a cibiyar ci gaban dimokuradiiya ta gidan Mambayya dake Kano, Mustapha Isyaku, ya ce kalubalen tsaro ya dade yana hana manoma zuwa gonaki.

Ya kuma ga baiken gwamnati na rashin tsare rayukan manoman a yankunan da abun ya shafa.

Malam Mustapha yMustaa bukaci gwamnati ta dauki matakin gaggawa wajen tabbatar da tsaro domin rage tasirin yunwa nan gaba, kamar yadda wasu masu hasashe daban-daban suka fara bayyana yiwuwar samun yunwa a kasar nan, sakammakon rashin tsaro, da barnar da ambaliyar ruwa ta haddasa a damunar bana.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci