OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yajin Aiki: Ministan Ƙwadago Ngige Ya Maka ASUU A Kotu

Yajin Aiki: Ministan Ƙwadago Ngige Ya Maka ASUU A Kotu

Ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ya maka kungiyar malaman jami’o’i zuwa kotun masana'antu ta Najeriya da ke Abuja, kan yajin aikin da kungiyar take yi.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa da aka rubutawa babban magatakardar kotun, a ranan 8 ga watan Satumba, 2022.

A cikin wasiƙar, Ngige ya zargi kungiyar ASUU da ƙin janye yajin aikin da ta fara tun a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022.

Ya buƙaci kotun da ta gaggauta sauraren lamarin domin kawo ƙarshen takaddamar da ke tsakanin kungiyar da gwamnati.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wasikar tana dauke da ƙorafi dangane da yajin aikin da ƙungiyar ta jima tana yi.

“Wannan shine takarda dake ɗauke da kwafi uku na asali dangane da taƙaddama tsakanin ma’aikatar ilimi ta tarayya da ƙungiyar ASUU domin yanke hukunci daga kotun ta Najeriya, kamar yadda wasikar ta karanta.

 “Wannan na ɗauke da aika tare da ikon da aka baiwa mai girma Ministan Kwadago da Aiki ta hanyoyin warware takaddamar da kuma tanadin sashe na 17 na dokar takaddamar da ake magana na Dokokin  Tarayyar Najeriya, 2004.

“Duba da yadda ‘yan kungiyar ASUU suka shiga yajin aiki tun ranar 14 ga Fabrairu, 2022 kuma sun ki yanke hukuncin duk da yarjejeniya da akayi, zan ji dadi idan aka gaggauta sauraron wannan takaddama domin a kawo karshen rigimar."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci