OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Yadda Sojoji Suka Kashe 'Yan Ta'adda Biyar a Kaduna

Yadda Sojoji Suka Kashe 'Yan Ta'adda Biyar a Kaduna

Hoto Daga: PremiumTimes

Sojojin Najeriya sun kashe wasu ‘yan ta'adda biyar a yunkurin su na kai hari wani kauye da ke yankin karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

An kashe 'yan ta'addan ne biyo bayan rahoton sirri da ya iske sojojin yayin da suke gudanar da aikin share fage.

'Yan ta’addan sun gamu da gamon su ne a hanyar su ta zuwa garin Fatika da ke karamar hukumar Giwa.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan ta’addan sun yi kokarin tserewa ne sakamakon matsin lamba da sojojin suka yi musu amma abin ya ci tura.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Litinin.

A cewar sa, an yi wa ‘yan ta’addan kwanton bauna ne a Kwanan Bataro inda aka kashe biyar daga cikin su a lokacin da suke batakashi.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya yaba wa sojojin bisa gaggawar da suka yi na tare 'yan ta'addan kafin su yi aika-aika.

Gwamnan kuma ya nuna jin dadin sa bisa aikin da aka gudanar.

Gwamnan ya kuma bukaci sojojin da su ci gaba da kokarin kawar da ‘yan ta’adda a yankin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci