OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Wani Matashi Da Dan Shekara 20 Sun Nutse a Ruwa A Kano

Wani Matashi Da Dan Shekara 20 Sun Nutse a Ruwa A Kano

Drown

Wani yaro dan shekara 12 mai suna Sadiq Isah ya rasa ransa a kauyen Jingabawa da ke karamar hukumar Minjibir a jihar Kano.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Jihar, a ranar jumma’a.

A cewar sa, “Mun samu kiran gaggawa daga Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) da misalin karfe 10:25 na safe cewa wani yaro ya nutse a tafkin ruwa kuma nan take muka aika da tawagar mu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 11:22 na safe.

“An fito da Isah daga cikin ruwan a sume kuma daga baya aka tabbatar da cewa ya mutu, yayin da aka mika gawar sa ga Hakimin Jingabawa, Malam Magaji Abdullahi.”

A halin da ake ciki, Abdullahi ya ce wani mutum mai shekaru 20 da ba a san ko wanene ba ya mutu a wani tafkin dake Ruwan Muni dake Kofar Nassarawa a karamar hukumar Municipal ta jihar kano.

“Anyi wa dakin kulawar mu kiran gaggawa a ranar 6 ga Oktoba, da misalin karfe 4:19 na yamma daga wani Ibrahim Nura, cewa wani mutum ya fada cikin tafkin ruwa, nan take aka  aika da tawagar mu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 4:22 na rana.

“Mun ceto wanda abin ya shafa a sume kuma aka garzaya da shi asibitin musamman na Abdullahi Wase dake Kano domin kula da lafiyar sa, daga baya wani likita ya tabbatar da mutuwar sa,” inji shi.

Abdullahi ya ce an mika wanda ya mutu ga ‘Dan  sanda Isma’ila Muhammad daga sashin ‘yan sanda na Kwalli Kano.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci